Abin Al'ajabi: Yan Gida Daya Sun Mutu Bayan Sun Ci Abinci Mai Dauke Da GubaMagidanci da matarsa da ke dauke da juna biyu tare da wani karamin yaro mai shekaru goma sun rasa rayukansu sanadiyyar cin abinci mai dauke da guba a unguwar Swali dake garin Yenegoa na jihar Bayelsa.


Rahoton ta bayyana cewa makota ne suka gano gawar matan mai suna Nkem Igwenta, Mijinta Orji Igwenta da kuma dan kaninta mai shekara goma Obinna Ogbani, har ma da wani bera da yacin abincin a macce a cikin daki.

Sai dai abin mamakin shine matar mai dauke da juna biyu ce ta shirya abincin, don haka aka rasa ta ya ya gubar ta shiga cikin abincin nasu, sai dai kwatsam aka tsinci gawarwakin nasu kwance a cikin dakinsu.


Wani dan kasuwa dake unguwar ya ce “Mummunan bala’I ya afka mana a titin winners, unguwar Swali, mun kadu sosai da mutuwar iyalai gaba daya.”

“Abin dake kara bamu mamaki shine ta yadda gubar ya shiga cikin abincinnasu, amma Allah zai saka musu idan har wani mutum ne yayi musu wannan muguntar.” Inji shi.

Rundunar Yansandan jihar ta bakin kakakinta, Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace Maigidan da mamatan ke haya a ciki ne ya kai karar abin al-ajabin ga yansanda.
Thanks For You Reading The Post We are very happy for you to come to our site. Our Website Domain name http://www.asknaija.com.ng/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a comment